fbpx
Friday, January 21
Shadow

Bai kamata kana hadamu da ‘yan ta’adda ba>>IPOB ga Sheikh Gumi

Haramtacciyar kungiyar dake neman kafa kasar Biafra,  IPOB ta caccaki babban malamin addinin Islama, Sheikh Gumi inda ta bayyana cewa bai kamata yanda yake hadasu da ‘yan ta’adda ba.

 

Kakakin kungiyar, Emma Powerful ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ga manema labarai.

 

Yace IPOB tana kasashe sama da 100 a Duniya kuma babu inda ake kiranta da sunan ‘yan ta’adda sai a Najeriya.

 

Kungiyar ta kara da cewa, ya kamata Sheikh Gumi ya boye fuskarsa cikin kunya saboda yanda yake goyon bayan masu kisan mutane.

 

Tace a baya ana ganin girman malamin amma a yanzi ya zubar da kimarsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *