fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Bam ya hallaka mutum 11 a kan iyakar Kamaru da Najeriya

Wani bam ya tashi a kan gadar El Beid, wadda ta raba iyakar kasashen Kamaru da Najeriya da ke garin Fotokol ya hallaka akalla mutum 11 kuma ya raunata 29.

Jami’ai a yankin sun tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua da faruwar lamarin, amma ba su bayar da cikakken bayani ba.
Ana zargin wasu ‘yan mata masu dakon kaya tsakanin Kamaru da Najeriya da haddasa wannan aika-aikar.
Kafafen yada labarai a Kamaru sun ruwaito cewa kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai harin.
Cikin wadanda suka jikkata har da wadanda suka fada cikin ruwa.
Kungiyar Boko Haram na ci gaba da kai hara-hare a yankunan da ke cikin kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi duk da rundunar hadin gwiwar da kasashen suka kafa don yaki da kungiyar.
A ranar Asabar ne kuma kasar Chadi ta bayar da sanarwar janye sojojinta daga Najeriya, wadanda ke cikin rundunar ta hadin gwiwa.
Masana na ganin janyewar za ta kara bai wa Boko Haram damar ci gaba da kai hari kan al’umomin yankunan da dama.
BBChausa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *