fbpx
Thursday, April 22
Shadow

Bama tare da Sunday Igboho>>Sarakunan Ogun

Sarakuna da matan Ogun sun bayyana cewa basa tare da me ikirarin kare muradun yarbasa da son kafa kasar Oduduwa,  watau Sunday Igboho.

 

Sarakunan sun bayyana hakane a matsayin goyon bayansu ga Alake of Egbaland, Oba Adedotun Aremu wanda tun can baya ya bayyana cewa baya tare da Igboho.

 

Oba Aremu ya dauki hankula bayan da ya fito yace zaman Najeriya a matsayin kasa daya ya fi Alheri fiye da raba ta, inda ya kara da cewa babu kasar da zata karbi ‘yan Gudun Hijirar Najeriya Miliyan 250 idan aka fara yaki.

 

Wannan dalili yasa gaba dayan Sarakunan yankin karkashin Basarake Bode Mustapha suka fito suka nuna goyon bayansu ga Oba Aremu tare da nemsanta kansu da Sunday Igboho.

 

Yace sun dauki wannan mataki ne saboda yanda aka san Yarbawa da goyon bayan gaskiya da kuma girmama na gaba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *