fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Bamu da alaka da cewa Sojoji na sayar da makamai a fagen yaki>>Hukumar Sojan Ruwa

Rundunar sojin Najeriya ta nesanta kanta da wasu kalamai da wata babbar jami’arta ta gabatar a gaban kwamitin tsaro na majalisar dokokin kasar da suka janyo ce-ce-ku-ce.

Ita dai Kwamado Jamila Abubakar ta yi zargin cewa akasarin haramtattun makaman da ake satar shiga da su kasar na da alaka da jami’an tsaron kasashe makwabta.

Ta halarci zaman kwamitin ne a matsayin wadda ta wakilci babban Kwamandan sojojin ruwan kasar Awwal Gambo, yayin wani zaman sauraron jin ra’ayin jama’a da kwamitin ya gudanar

Sai dai cikin wata sanarwar da rundunar sojin ta fitar a hukumance, ta ce ba da yawunta jami’ar ta furta wadannan kalamai ba, bilhasali ma ra’ayinta ne kawai ba na rundunar ba.

A maimakon hakan rundunar ta yaba da kokarin kasashen da ke makwbataka da Najeriya ta fuskar hadin ka da suke bayarwa wajen kawar da makaman.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *