fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Bamu da wata yarjejeniyar sayen makamai ta Dala Miliyan $875 da kasar Amurka>>Gwamnatin Tarayya

Ministan yada labarai da Al’adu, Lai Muhammad ya bayyana cewa, Najeriya bata san da wata yarjejeniyar sayen makamai da kasar Amurka ta Dala Miliyan $875 ba.

 

Ya bayyana hakane a yayin da ake rade-radin cewaz ‘yan Majalisar kasar Amurka sun ki amincewa da sayarwa da Najeriya makamai da wadannan makudan kudade saboda zargin Gwamnatin na take hakkin bil’adama.

 

Lai Muhammad yace banda Jiragen Super Tucano 12 wanda yanzu haka an kawowa Najeriya 6 daga ciki, babu wata yarjejeniyar dake tsakanin kasashen biyu.

 

Ya kara da cewa kuma alakar Najeriya da kasar Amurka bata da tangarda.

“There is no contract of arms between the Federal Republic of Nigeria and the United States of America today apart from the 12 Super Tucano Attack Helicopters of which six had been delivered. We are quite satisfied with the progress and cooperation that we received from the government of the US on this issue.”

“As a matter of fact, six of the Tucano helicopter will be launched on Aug. 3, this year.”

“We are not aware of the so-called 875 million USD arms contract or some helicopters which they said some lawmakers in the US are trying to persuade the president of the US not to honour. The relationship between Nigeria and the US is smooth and waxing stronger,” he said

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *