fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Bamu kaiwa Abba Kyari da aka dakatar Ziyara ba>>Gwamna Zulum da Shettima

Wani Bidiyo dake yawo a shafukan sada zumunymta ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum da tsohon Gwamnan Jihar, Kashim Shettima, sun kaiwa dansanda, DCP Abba Kyari da aka dakatar ziyara.

 

Rahoton yayi zargin cewa, sun kaiwa Kyari ziyara ne dan nuna masa suna tare dashi akan abinda ya sameshi.

 

Ana Zargin Abba Kyari da alaka da dan Damfarar nan da kasar Amurka ta kama, watau Hushpuppi.

 

Saidai Kyari ya karyata alaka dashi. Gwamna Babagana Umara Zulum ta hannun kakakinsa, Isa Gusau ya bayyana cewa Gwamna Zulum da Shettima basu zan gidan Abba Kyari ba ballantana ma su kai masa ziyara.

 

Yace Bidiyon da ake gani, tsoho ne wanda Kyari da mutanensa suka kaiwa Shettima ziyara a yayin da aka rika yada jita-jitar cewa wai ya mutu a kasar UK.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *