fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Bamu yadda da bayaninka ba, kawai ka sauka ko kuma Buhari ya koreka>>Wasu Masana daga kudu kan harkar Tsaro ga Pantami

Wasu Masana kan harkar tsaro sun bayyana cewa, bayanin da Sheikh Pantami yayi akan kalaman da daya taba yi a baya kan kungiyoyin Alqaeda da Taliban bai gamsar ba.

 

Sun bayyana cewa, kodai ya sauka da kansa ko kuma Shugaba Buhari ya saukeshi, saboda wadancan kalaman masa sun yi nauyi da yawa.

 

Ministan Sadarwa, da Tattalin Arzikin Zamani yayi bayanin cewa yana dan shekaru 13 ya fara wa’azi, amma bayan da ya girma ya kara Ilimi ya canja akan ra’ayoyin da yake dasu akan irin wadancan ra’ayoyi nasa, kamar yanda Daily Trust ta bayyana.

 

Wani tsohon sojan kasar Amurka, Bishop Johnson ya bayyana cewa kamata yayi kawai Pantami ya yi Murabus ko kuma Shugaba Buhari ya saukeshi. Yace masu ra’ayin ta’addanci ba kasafai suke canja halaiyarsu ba. Dan hakane yace kawai tunda abin ya zamo har yana neman taba gwamnatin tarayya, kamar yanda aka yi da tsohuwar ministar Kudi, Kemo Adeosun kan takardar Bautar kasa, Shima Pantami ya sauka.

 

Shima dai Shugaban kungiyar masu kula da tsaro da aikata manyan Laifuka a Najeriya, Williams Ekposon ya bayyana cewa bayar da hakurin Pantami bai isa ba, kamata yayi ya ajiye mukaminsa.

 

Punchng ta ruwaito cewa, shima dai wani kwararre a bangaren tsaro a Legas, Dickson Osagie ya bayyana cewa, abinda kawai ya dace Pantami yayi shine yayi murabus.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *