fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Bamu yadda dan Arewa ya tsaya takarar shugaban kasa ba a 2023>>Ohanaeze Indigbo

Kungiyar kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta bayyana cewa bata yadda dan Arewa ya tsaya takarar shugaban kasa ba a shekarar 2023.

 

Itama kungiyar jihohin tsakiyar Najeriya ta hau wannan matsayi na Ohanaeze.

 

Kwankwaso, Atiku, da Tambuwal na cikin wanda ake ganin zasu tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023 daga Arewa.

 

Saidai kungiyar ta Ohanaeze Indigbo tace kowace jam’iyya kamata yayi ta tsayar da dan takarar shugaban kasa daga kudu.

 

Kungiyar tace kundin tsarin mulkin Najeriya bai dace da kasar ba saboda babu adalci a cikinsa, ya kamata a sake wani.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *