fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Ban Ga Dalilin Cigaba Da Tsare Mahaifina Ba, Domin Laifin Da Ake Ce An Riƙe Su Saboda Da Shi An Saki Duk Wanda Ake Tuhuma Saboda Rashin Hujja>>Suhaila Zakzaky

A wata hira da BBC Hausa Suhaila Ibrahim ta ce ba su da wani buri da ya wuce su ga an saki mahaifansu sun sake rayuwa da su.

A ranar Alhamis 3 ga watan Yunin 2021 ne Malam Ibrahim ya cika kwana 2,000 a hannun gwmanatin Nijeriya, tun bayan kama shi da aka yi tare da matarsa a Disamban 2015 a gidansa da ke Zaria.

Tun daga wancan lokacin mabiyansa suke ta kira ga gwamnati da ta sake shi, musamman bayan bayar da belinsa da kotu ta yi.

“Babban fatanmu shi ne a sake su, tun da shi kansa laifin da aka ce an riƙe su a kai to an saki duk wani da ake tuhuma da shi, an ce saboda babu hujja.

“To don me kuma za a ci gaba da riƙe su da aka ce su suka sa a aikata laifin?” a cewar Suhaila.

Ta ƙara da cewa a yanzu ma an kai matakin da ba a barinsu su ga iyayens nasu akai-akai kamar da.

Sannan ta yi ikirarin har yanzu akwai raunuka na harbinsu da aka yi lokacin da aka je tsare su da ba su warke ba, “kuma ba a mayar da hankali wajen ba su kulawar da ta dace ba.”

“Rayuwarmu (ƴaƴansu) cikin waɗannan kwanakin na tattare da tashin hankali da wahala saboda raba mutum da iayye ba za a iya haɗuwa a lokacin da ake so ko nkulawa da su ba, abin tashin hankali ne.

“Balle su a irin yanayin da aka ɗauke su,” ta ƙara da cewa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *