fbpx
Monday, November 29
Shadow

Ban ji dadin mutuwar mutanen da gini ya fadawa a Legas ba>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, bai ji dadin yanda gini ya fadawa wasu mutane suka mutu a Legas ba.

 

Gini me hawa 22 ne ya fadi a Legas inda mutane akalla 10 suka rasa rayukansu.

 

Shugaban yace yana mika sakon ta’aziyyar sa ga iyalan mamatan sannan kuma yana baiwa hukumomin da alamarin ya shafa umarnin su bayar da taimakon da ya dace.

 

Hakan na kunshene a cikin sanarwar da shugaban ya aike ta bakin kakakinsa, Malam Garba Shehu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *