fbpx
Friday, April 23
Shadow

Ban yi karar Atiku ba>>Babban Lauyan Gwamnati

Bayan da suka da caccaka ta yi yawa akan karar da ake zargin ya shigar kan cewa Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ba dan Najeriya bane, Babban Lauyan Gwamnati, Abubakar Malami ya bayyana cewa bai Shigar da kara akan Atiku ba.

 

Malami ya musanta hakane a wata sanarwa da ya fitat ta hannun kakakinsa, Umar Jibril Gwandu.

 

Yace wannan abune da aka yi shi tun Shekarar 2019 amma yanzu an daukoshi ana yamadidi dashi kamar wani Sabon Labari.

 

Yace Jam’iyyar APC ma a nata bagaren ta shigar da irin wanna kara inda take cewa Atiku ba dan Najeriya bane Asalinsa.

“The issue had already been widely reported by the media since April 2019. It is unfortunate that stale news stories capable of causing confusion are repackaged and presented to the general public as current news.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *