fbpx
Monday, November 29
Shadow

Ban ziyarci Buhari don siyasa ba – Tinubu

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a ranar Lahadi ya karbi bakuncin jagoran jam’iyyar APC mai mulki Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa, Abuja.

Sun yi ganawar sirri.

A karshen ganawar, Tinubu ya ce ya je fadar shugaban kasa ne domin ya gode wa shugaban da ya ziyarce shi a Landan inda ya nemi magani.

Ya jaddada cewa taron ba shi da wata manufa ta siyasa.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ganawar, Tinubu ya ce: “Na zo ne domin in gode wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ziyarce ni a Landan lokacin da aka yi min tiyata a gwiwa. Ya nuna tausayi. Shi shugaba ne na musamman.”

Ya kara da cewa: “Sai dai in gode wa shugaban kasa, da farko, saboda ziyarar da ya kawo min a gidana da ke Landan bayan tiyatar da aka yi min, da kuma yi min fatan alheri, ya kara min kwarin guiwa da kuma abin da shugaba na kwarai zai yi don hada kai. Don haka, abin da yasa na zo ne da kuma yi masa barka da dawowa daga tafiyar Saudiyya.

A martanin da shugaban ya mayar, tsohon gwamnan jihar Legas, ya ce shugaban ya ji dadin kasancewarsa a kusa da shi, inda ya ce bai wajaba ya yi magana kan sauran abubuwan da suka tattauna ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *