fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Bani da niyyar komawa APC>>Gwamna Fintiri

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya musanta rahotannin da ke cewa zai fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC sakamakon rikicin shugabanci a matakin kasa da jam’iyar ta fada ciki kwanakin da suka gabata.

A kwanakin baya ne dai aka yi ta yaɗa jita-jitar cewa gwamnan na da ra’ayin komawa jam’iyya mai mulki ta APC, kamar yadda gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya koma APC daga PDP.

Sai dai a hira da Fintiri ya yi da BBC, ya bayyana cewa: “Lokacin da take da ma’ana, ina da buƙata ma ban je ba ballantana yanzu da ta lalace, ai jam’iyyar APC ta zama lalatacciyar masar da ko almajiri ba ya buƙat.”

Gwamnan ya bayyana cewa zai ci gaba da bayar da gudunmawa wurin gina jam’iyyar PDP inda ya ce suna fatan jam’iyyar ta su ce za ta samar da shugaban ƙasa a shekarar 2023.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *