Jarumin masana’antar shirya fina-finai ta Kudu (Nollywood), Frank Donga ya bayyana cewa barin Najeriya zuwa wasu kasashe baya sa mutum ya zama mai arziki.
Haka zalika, zama a cikin kasar ba shi ne kishin kasa ba.
Frank Donga ya bayyana hakan ne a cikin shafinsa na Twitter, kuma a karshe yayi wa kowa fatan alheri akan abunda suka sa gaba.