fbpx
Monday, November 29
Shadow

Bayan Biyan Diyya, dole a hukunta wanda suka kashe Hausawa a Oyo, Kuma Gwamnonin Yarbawa ne suka tunzura fadan>>Kakakin Majalisa

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Ahmad Lawan, ya ce dole ne sai an hukunta waɗanda suka kashe mutane yayin rikicin baya bayan nan da aka samu tsakanin Hausawa da Yarbawa a jihar Oyo, da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Yayin wata hira da BBC Ahmad Lawan ya ce baya ga biyan diyyar rayukan da aka yi asara da gwamnatin jihar ta lashi takobin yi, kamata ya yi a gudanar da bincike don gano waɗanda suka haifar da tashin hankalin a kuma gurfanar da su a gaban kotu, domin su girbi abin da suka shuka.

“Abin da ya faru a Oyo da kuma wasu jihohin kudancin Najeriya an samu rashin shugabanci, ba zan ce na gwamnoni kaɗai ba, amma dai su suke da muhimmin haƙƙi na kare mutane, kuma irin kalaman da wasu daga cikinsu suka rika yi sun haifar da tunzura al’ummar waɗannan jihohi, sai suke ganin kamar jagororinsu na goya musu baya, suka ɗauki wannan mataki,” inji shugaban Majalisar Dattawan.

Ya ƙara da cewa Majalisar Dattawan ta yi muhawara dangane da wannan al’amari bayan kammala hutunta, sannan ta yi Allah wadai da abin da wasu shugabanni na siyasa ke yi na kalaman tunzura al’umma.

A cewarsa, shi ma shugaba Muhammadu Buhari ya zauna da gwamnonin ƙasar baki daya, kuma ya faɗa musu cewa ba a yadda wani gwamna ya je ya riƙa yin kalaman da za su janyo tashin hankali da kuma tarzoma a jiharsa ba.

”Ya shaida musu cewa tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowanne ɗan ƙasa damar zama a duk inda yake son ya rayu, don haka baza a lamunci wani ya ce zai kori wasu daga jiharsa ba saboda ba ƴan jihar ba ne,” in ji shi.

”Eh, a biya diyya, amma a tabbatar da cewa ba a kashe mutane a banza ba, ba wai kawai kayan da aka ƙona da waɗanda aka kashe shikenan ba, a bi musu kaadi, ko an biya diyya a nemo waɗanda suka yi wannan abu, jami’an tsaro su kama su a kai su kotu a hukunta su, wannan ne kaɗai zai hana wasu aikata irin hakan a nan gaba,” a cewarsa.

Wani mutum mai suna Rabi’u da ya ga yadda lamarin ya faru dai ya shaidawa BBC tun a lokacin cewa rikicin ya faro ne bayan da ‘yan bangar Yarabawa suka samu labarin cewa wani Bahaushe ya kashe ɗan uwansu beyerabe, shi ya sa suka “riƙa shiga gida-gida inda Hausawa suke da zama suna kai musu hari”.

“Mutanen rike da bindigogin da aka yi da ɗan boris sun fito daga yankuna irin su Bodija, Mokola duka a Ƙaramar Hukumar Akinyele, sun ƙone shaguna sama da 250 a kasuwar Shasha, wasu ma na ‘yan uwansu ne Yarabawa. Kazalika sun riƙa tare hanya suna kashe Hausawa,” in ji shi.

Rabi’u ya ce abokansa biyu ‘yan asalin Jihar Kano da Sokoto suna cikin waɗanda aka kashe abin da ya sa shi da wasu mutane suka ruga gidan Sarkin Shasha domin neman mafaka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *