fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Bayan Kashe matasa saboda zargin satar Kaza, Kotu ta dauki babban mataki akan hukumar ‘Yansanda a Bauchi

Wata Kotun Tarayya a Bauchi ta umarci ƴan sandan Najeriya su biya diyyar naira miliyan 210 kan kashe wasu mutane biyu bayan azabtar da su da jikkata mutum guda kan zargin satar kaza.

Abdulwahab Bello da Ibrahim Babangida da Ibrahim Samaila, an cafke su tare da lakada musu duka a watan Yulin shekarar da ta gabata, kan zargi satar kazar wani tsohon ɗan sanda.

Azabtar da su da aka yi, ya kai ga Samaila da Babangida sun mutu, yayinda Bello ya tsira da muggan raunuka da ke barazana ga rayuwarsa. Bello ya shigar da ƙara da neman diyyar naira miliyan 150 ga kowanne daga cikinsu.

Jaridar Punch ta rawaito cewa alkalin da ya yanke hukuncin ya ce laifukan da aka aikata sun take hakkinsu kamar yada ya ke ƙunshe a kudin tsarin mulkin Najeriya.

Sanna ya ƙara cewa abin da ƴansanda suka aikata zulunci ne da gidadanci.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *