fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Bayan sojoji 10 da suka yi garkuwa dasu, Tsageran ‘yan Bindiga sun kuma sace dansanda a jihar Imo

Tsageran ‘yan Bindiga da ake zargin ‘yan IPOB ne sun sace wani dansanda a ofishin ‘yansanda dake Mbieri dake karamar Hukumar Mbaitoli ta jihar.

 

Lamarin ya farune da misalin safiyar Ranar Alhamis. Sun budewa ofishin ‘yansandan wuta inda akai bata kashi amma daga baya ‘yansandan suka tsere, kamar yanda wata majiyar tsaro ta gayawa Punchng.

 

Saidai sun kama daya daga cikin ‘yansandan suka tafi dashi. Sun kuma kwashe wayoyin da suka tarar da kuma sakin duka masu laifi dake tsare.

 

A jiya ne dai muka ji daga TheCable yanda tsageran ‘yan Bindigar suka sace wasu sojoji 10 sukawa 5 daga ciki gunduwa-gunduwa.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *