fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Bayar da Gudummawar miliyan N50 ga jihar Buhari ba zai saya muka tikitin APC ba>>Bamgbose ga Tinubu

Olusegun Bamgbose, Coordinator na kungiyar CAGG, ya bayyana gudummawar naira miliyan 50 da shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Tinubu ya yi wa jihar Katsina a matsayin siyasa, munafunci da takaici.

 

Bamgbose ya ce ba laifi ba ne a ba da gudummawar kudi don taimaka wa ’yan kasuwar da suka yi asarar kayayyakinsu da shagunansu a babbar kasuwar ta Katsina, amma yana mamakin dalilin da ya sa tsohon Gwamnan na Jihar Legas bai taba tunanin yin hikima da wajibcin yin hakan ba lokacin da rikici ya faru a Kasuwar Sasa a jihar Oyo.

 

Ya kuma yi mamakin dalilin da ya sa halin ‘yan kasuwar da kayansu da dukiyoyinsu suka salwanta a gobarar Kasuwar Ijesha bai taba daukar hankalin Tinubu ba.

 

A baya dai hutudole.com ya kawo muku yanda Bola Ahmad Tinubu Ya kai ziyara Katsina tare da bada tallafin Miliyan 50  Ga wadanda gobarar kasuwar jihar ta rutsa dasu, wanda daga baya lamarin ya jawo cece-kuce.

Bamgbose ya ce “yana da lokacin tashi zuwa jihar ta Katsina don kai wa wadanda lamarin ya rutsa da su ziyarar ta’aziyya amma bai taba samun lokacin da zai ziyarci jihar Oyo ba ko ma kasuwar Ijesha ta jihar Legas,” in ji Bamgbose.

 

“Mai yiwuwa ya ba da gudummawar N50m din kuma da kansa ya ziyarci jihar Katsina don burge ko gamsar da Buhari wanda ya fito daga jihar Katsina, wannan siyasa ce ta yara kuma bai dace ba.

 

“Wannan aikin sadaka bai isa ba ganin cewa mutane sun riga sun san dalilansa na irin wannan kyautar. Ku bari a sanar da shi cewa gudummawar da zai bayar ba zai sa ya zama abin kauna ba idan aka zo zaben fidda gwani na APC a 2023.

 

“Har yanzu APC ba za ta hana shi tikiti ba. MKO Abiola yayi fiye da shi har yanzu National Party of Nigeria, NPN bata da wani shiri na bashi tikitin takara. Farantawa Arewa rai ba shine sirrin zama Shugaban Najeriya ba, gara ma farantawa talakawa rai.

 

“Gudummawar da yake bayarwa ba za ta iya sauya tunanin jam’iyyar ba. Gara ya manta da burinsa na Shugabancin kasa, mafarki ne kawai wanda kila ba zai cika ba. Najeriya na fatan samun shugaban da zai fito fili a 2023, “in ji shi.

 

 

“He had time to fly to Katsina State to pay the victims a sympathy visit but never had time to visit Oyo State or even the Ijesha market in Lagos State,” Bamgbose noted during a chat with DAILY POST.

“He possibly must have donated the N50m and personally visited Katsina State to impress or appease Buhari who is from Katsina State, this is politically childish and inappropriate.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *