fbpx
Monday, October 25
Shadow

Bazan iya fallasa sunayen masu daukar nauyin Boko Haram ba, abune na Sirri>>Shugaban EFCC

Shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa ya bayyana cewa ba zai iya fadar sunayen masu daukar nauyin ayyukan Boko Haram ba.

 

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda wakilin gidan talabijin din ya tambayeshi cewa ga kasar UAE ta fallasa masu daukar nauyin ta’addanci, shin me zai hana gwamnatin Najeriya ma ta yi haka?

 

Bawa yace ba zai iya bayyana sunayen wanda ke daukar nauyin ta’addancin ba dan kuwa abune na sirri.

 

Yace amma suna aiki tukuru tare da sauran hukumomin gwamnati da kuma kasashen waje dan ganin an yi maganin matsalar.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *