fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Bennett ya maye Netanyahu a matsayin Firaministan Isra’ila

Benjamin Netanyahu ya rasa ikonsa na shekaru 12 kan mulkin Isra’ila bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri’ar amincewa da sabuwar gwamnatin haɗaka.

Naftali Bennett na jam’iyyar Yamina zai jagoranci sabuwar “gwamnatin ta canji.”

Shi zai jagoranci gamayyar jam’iyyun da suka samu rinjayen ƙuri’a ɗaya wanda ya kai ga kawo ƙarshen mulkin Netanyahu.

Mr Bennett zai zama Firaminista har zuwa watan Satumban 2023 ƙarƙashin tsarin karɓa-karɓa.

Daga nan zai miƙa mulki ga Yair Lapid, shugaban jam’iyyar Yesh Atid, na tsawon shekara biyu.

Mista Netanyahu – wanda ya fi daɗewa kan mulki a Isra’ila ya mamaye siyasar Isra’ila na tsawon shekaru.

Yanzu zai kasance shugaban jam’iyyarsa ta Likud kuma jagoran adawa.

Lokacin da ake tafka mahawara a majalisa, Mr Netanyahu ya yi alwashin cewa: “Za mu dawo.”

Tuni shugaban Amurka Joe Biden ya aika da sakon taya murna ga Mista Bennett, yana mai cewa a shirye yake ya yi aiki tare da shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *