fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

Benuwe ba ta cikin Biafra – Gwamnatin Jihar ta gargadi Nnamdi Kanu

Gwamnatin Jihar Benuwe ta gargadi shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu da kungiyar tsaro ta Gabas (ESN) kan cewa su fitar da Jihar daga yankin Biafra.

Wannan ya biyo bayan barazanar da Kanu ya yi kwanan nan na aika mambobin ESN don kare ‘yan kabilar Ibo da ke zaune a Benuwe.

Kanu ya bayyana kananan hukumomin Ado da Oju a matsayin wuraren da suke bukatar jami’an tsaro ESN.

A martanin Shugaban karamar hukumar Ado, James Oche, ya fadawa manema labarai a ranar Asabar cewa, yankin jihar ba zai taba zama karkashin Biafra ba.

A karshe ya kara da cewa Gwamnatin Jihar tana gargadi Nnamdi Kanu da hukumar tsaro ta ESN da su dai na alakanta yankunan Jihar da Biafra.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *