fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Bernardo Silva ya dusashe Messi, Neymar, da Mbappe ya dauki hankula sosai a wasan da Manchester City ta lallasa PSG 2-1

Wasan Champions League da aka buga tsakanin Manchester City da PSG ya kare da sakamakon 2-1 inda City ta yi nasara.

 

Kylian Mbappe ne ya fara ciwa PSG kwallo ta farko bayan dawowa daga hutun rabin lokaci saidai ashe ya ciwo me ‘ya’ya.

 

Raheem sterling da Gabriel Jesus sun ciwa City kwallaye 2 wanda a haka aka tashi wasan 2-1.

Duk da cewa, Lionel Messi,  Neymar da Kylian Mbappe na cikin filin amma kokarin Bernardo Silva ya dusashe tauraruwarsu.

Ya sha yabo sosai inda bayan wasan shine ya zama gwarzon wasan na jiya kuma aka damka masa kyauta, wani yaro ya sameshi inda ya rokeshi ya bashi kyautar rigarsa kuma ya bashi din.

 

Silva ya taba kwallon sai 54 a wasan na daren jiya inda kuma duka babu wadda ta fita daga kafarsa ba tare da yayi abinda yake so da ita ba.

 

Ya dauko kurosin guda 2, ya taimaka an ci kwallo sau 1.

A wani Rahoto na daban me alaka da wannan kuma, an samu cewa, PSG tace kocinta, Mauricio Pochettino.

Da yawa dai sun rika mamakin yanda ga Neymar, Messi da Kylian Mbappe amma City ta yi nasara a wannan wasa.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *