fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Bidiyo Da Duminsa:Kalli yanda Kungiyar Hamas ta jefawa kasar Isra’ila Rokoki 200 a matsayin martanin cin zarafin Falasdinawa

Kungiyar Hamas ta jefawa Kasar Isra’ila Rokomi 200 a matsayin wani martani kan hare-haren da kasar ke kaiwa kan Falasdinawa.

 

Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Isra’ila ta rika kaiwa Falasdinawa hare-hare har a cikin masallacin Al-aqsa yayin da suke sallah.

 

Saidai kasar ta Isra’ila tace dole ta kare jama’arta inda tace ta mayar da martani inda ta kashe ‘yan Kungiyar Hamas 15 da kjma lalata wasu daga cikin sansanin ‘yan kungiyar.

 

Hakanan hukumar Tsaro ta kasar Isra’ila tace ta kuma lalata ma’ajiyar makamai ta hamas da kuma wajan kera makaman.

 

 

Hakanan kasar Isra’ila tace ta kai hare-hare 130 kan kungiyar Hamas, ciki hadda wanda ta kai kan shugaban kungiyar.

 

Ma’aikatar harkokin kasar wajen Isra’ila ta bayyana cewa rokoki 200 ne Hamas ta harbawa a ranar Litinin kawai.

 

Ta kuma wallafa yanda harin ya kasance a shafinta na sada zumunta.

 

 

 

 

 

Reuters ta ruwaito cewa, mitane 20 ne harin da Isra’ila ta kaiwa Falasdinawa ya kashe, viki hadda yara 9.

 

https://twitter.com/cjwerleman/status/1391934828832968704?s=19

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *