fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Bidiyo: Musulman Najeriya sun maida martani kan bidiyon wata mata mai wa’azin musulinci tana kwaikwayon fastoci wajen fitar da aljanu da cutukka ga mutane

Wasu Musulman Najeriya sun mayar da martani kan bidiyon wata mata musulma mai wa’azi tana kwaikwayon fastoci wajen fitar da aljanu da cututtuka.

Masu amfani da Facebook da suka mayar da martani ga bidiyon, sun bayyana cewa wannan ba koyarwa addinin Musulunci ce ba kuma alama ce ta ƙarshen zamani.

Wata Asiyah Aisha Alubankudi wacce ta raba bidiyon, ta rubuta;

Wannan abin kunya ne, banso wallafa wannan bidiyon ba amma dole ne a ɗauki mataki da sauri.

Yakamata a yiwa wannan matar gargaɗi nan da nan kafin ta fara yaudarar matasa masu ruɗu.

Wannan ba lamari ba ne da za’ayi shiru, ya kamata Limamanmu su sa baki cikin gaggawa.

Kalli bidiyo a kasa…

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *