fbpx
Monday, May 10
Shadow

Bidiyo; Wata yarinya yar bariki ta watsawa dadurunta zazzafan mai ga jiki a Abuja

Wata yarinya yar bariki ta watsawa dadurunta soyayye ko zazzafan mai ga jikinsa a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Lamarin ya faru ne sakamakon wata yar matsala da suka samu a tsakaninsu, wanda hakan yasa tayi masa wannan aika-aikar.

An bayyana cewa yarinya a lokacin da dadurun nata wanda magidanci ne kuma mai iyali ya shiga ban daki a lokacin da suke tare sai ta shiga wajen dafa abinci inda ta dumama mai kuma yana fito ta watsa masa.

Kururuwar da yayi yasa mutanen da ke kusa sun kawo masa dauki tare da rike yarinyar.

Har yanzu ba a bayyana dalilin da yasa yarinyar tayi masa hakan ba, amma nan bada jimawa zamu kawo maku cikakken rahoto.

Kalli bidiyon a kasa;

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *