fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Bidiyo ya bayyana dake nuna yanda kasar Iran ta harbo jirgin sama daya kashe mutane 176 bisa kuskure da tunanin cewa Amurka ce ta kawo mata hari

Hujjoji sun fara bayyana dake da alamar tabbatar da ikirarin kasar Amurka na cewa kasar Iran ce ta harbo jirgin kasar Ukraine da ya kashe mutane 176 bisa kuskuren tunanin kasar Amurkace ta kai musu hari.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kasar Ingila ma ta rufawa kasar Ta Amuka baya akan wannan zargi.

Wani bidiyo da shafin bincike na shahararrun “yan jaridu, Bellingcat ya samu ya nunabyanda wani mutum ya dauki bidiyon dake nuna yanda makamin Roka ya bugi jirgin kamin daga baya ya fado kasa.

Wasu sun yi tambayar cewa ya akai mutumin yasan cewa abin zai faru har ya dauki wayarshi ya nadi hoto?

Wanda suka tantance bidiyon sun bayyana cewa, ana tunanin makamin da aka harbi jirgin dashi biyune, da mutane suka ji karan na farko sai suka fito waje suka fara daukar hoto a wannan lokacinne aka harba makami na biyu.

Itama dai kafar watsa labaran kasar Amurka ta CBS ta samu wani bidiyon kyamarar kan titi ta CCTV data nuna yanda ake zargin an harbi jirgin da makami kuma ya tarwatse.

Kasar Iran dai ta karyata wannan zargi da ake mata inda tace da harbin jirgin ta yi ta yaya za’ace matukin jirgin yayi kokarin komawa filin jirgin kamin jirgin ya fadi kasa.

Saidai a bangare daya kuma kasar ta Iran ta ce atafau ba zata bayar da na’urar dake nadar abinda ke faruwa a cikin jirgin ba ta Black Box dan ayi binciken ainahin dalilin faduwar jirgin. Wannan yasa mutane da dama ke tunin zargin na kasar Amurka ka iya zama gaskiya.

Faduwar jirgin ta zo ne daidai lokacin da Iran ke ruwan bama-bamai na tamuwar gayya akan sojojin  kasar Amurka kan kisan janar din sojanta, Qassem Soleimani da kasar ta yi


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *