fbpx
Friday, May 14
Shadow

Bidiyo:Kalli yanda Matasa suka daure wani a jikin Itaciya suka zaneshi sosai bayan dukan rashin Mutunci da yawa wata Tsohuwa

A bidiyon, an ga mutumin yana amfani da doguwar sanda yana yi wa tsohuwar bulala, ya kada ita ƙasa, ya cigaba da dukanta.

An bayyana mutumin a matsayin Sunday Maduegbunam Kosisochukwu daga Ogidi a jihar Anambra.

An ga makwabta suna rokonsa amma sam yayi burus da maganarsu ya cigaba da dukanta.

Saidai matashi ya gamu da fushin matasan garin bayan da suka ga bidiyon, suka kuma tambaye ko da gaske shine a bidiyon? Ya amsa cewa shi ne tare da neman gafararta.

Duk da hakan matasan sun hukunta shi ta hanyar taure hannayensa da kafafunsa kan icce, kuma sukai ta zabga masa bulala.

Kalli bidiyon a kasa;

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *