fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Bidiyon Sanata Uba Sani Tsirara: Duk Muna yin irin wannan abu saidai wani ya fi wani kiyayewa>>Cewar Wani Sanata


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Bayan bayyanar bidiyon sanatan mazabar Kaduna ta tsakiya, Sanata Uba Sani a shafukan sada zumunta kusan kwanaki 2 da suka gabata da abin ya watsu kamar wuyar daji, wasu abokan aikinshi sun yi martani akai.

A bidiyon an ga sanatn ya fito daga bayi yana goge kanshi da tawul.

An nunawa Abokan aikinshi sanatoci da yawa wannan bidiyi inda suka bayyana cewa wannan ai bai sabawa dokar aikinshi ba kuma da alama wanine ke son bata masa suna.

Sun kuma bayyana cewa ba zasu tuhumi sana Uba sanin ba akan wannan lamari.

The Nations ta bayyana cewa daya daga cikin sanatocin ya fadi cewa dukansu fa suna wannan abin amma dai wasu sun fi wasu kiyaye wane, inda ya kara da cewa wasu suna da yarda da yawane.

Rahoton ya kara da cewa, bayan fitowar bidiyon, sanatoci da yawa sun je wajan Uba Sani inda suka jajanta mai.

Ya kuma ce sanatocin sun bayyana cewa abune da ya shafi rayuwarshi ba aikinshi ba dan haka ba zasu hukuntashi ba.

Saidai sun rika tambayar sin ko wanene ya fitar da wannan bidiyon, ssnnan ya akai sanat guda ya yadda aka dauki irin wannan bidiyo nashi sannan yayi sakaci dashi?

Akwai fargaba a wajan bangaren Sanata Uba Sani kan cewa watakila akwai sauran Bidiyon nashi da ake shirin saki nan gaba.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *