fbpx
Monday, September 27
Shadow

Bidiyon Sheikh Pantami da matar shugaban kasa, A’isha Buhari ta saka ya dauki hankulan ‘yan Najeriya

‘Yan Najeriya da dama suna ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan wani bidiyo da uwargidan Shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta wallafa a shafinta na Instagram, da ke nuna Sheikh Isa Ali Pantami yana kuka bayan wata ayar Al-Kur’ani da mai jan baƙinsa ya karanta.

A kasan bidiyon da ta wallafa ranar Lahadi, Aisha Buhari ta wallafa saƙon da ke cewa “Tunatarwa: A cire tsoro a yi abin da ya dace.” Sai dai daga haka ba ta yi wani ƙarin bayani ba.

Mai jan baƙin Ministan Sadarwar ya jawo aya ta 63 ne daga cikin Suratu Maryama inda Allah SWT ke cewa: “Waccan Aljannar ce wadda Muke gadar da wanda ya kasance mai aiki da takawa daga bayiNa.”

Bayan janyo ayar ne da shi ma mai jan bakin ya yi cikin kuka, sai Sheikh Pantamin ya sunkuyar da kansa ƙasa yana shesshekar kuka yana cewa “Allahumma ja’alna minhum” har sau uku. Wato yana addu’a ne cewa “Allah Ka sa muna daga cikinsu.”

Amma Aisha Buhari ta rufe sashen yin tsokaci a karkashin bidiyon, ta yadda babu wanda zai iya cewa komai.

Babu wanda zai iya bugar kirji ya fadi ko me Aisha Buhari take nufi da wannan saƙo nata, amma a iya cewa ta yi shi ne a lokacin da Najeriya ke fama da mataloli iri-iri musamman ta fannin tsaro, inda ‘yan kasar da dama ke dora laifin hakan da gazawar gwamnati.

Daga baya a ranar Litinin da misalin karfe 12 na rana, sai ta sake wallafa bidiyon da sakon da ya fi na baya tsayi, inda ta ce: “Tafsir na Malam kan tsoron Allah ba tsoron mutum ba!

“Da aka cire tsoro da son kai aka shiga Jihar Zamfara, abubuwa sun fara kyau. Sai a dage a shigo sauran wurare da ke bukatan haka.”

Tuni dai wasu jaridun Najeriya da wasu masu amfani da shafukan sada zumunta (Bloggers) suka wallafa labarin, al’amarin da ya jawo mutane suka samu kafar bayyana ra’ayoyinsu.

Shafin Hausaa_Fulanii da na Insidearewa Instagram sun wallafa saƙon a shafukansu, inda suka bai wa masu bibiyarsu damar bayyana ra’ayoyinsu.

Mutane da dama a shafukan sada zumunta sun yi ta fassara saƙon da cewa tana yi wa Sheikh Pantami shaguɓe ne, duba da cewa yana daga cikin na hannun daman Shugaba Buhari, kuma ita an san ta yi ƙaurin suna wajen sukar lamiran wasu abubuwa na maigidan nata a baya.

Kusan ma dai za a iya cewa duk sakonnin da muka bibiya sun yarda 100 bisa 100 cewa Aisha shaguɓe ne take yi wa Sheikh Pantami, sai dai wasu ɓangaren na goyon bayanta kan “tsage gaskiya da take yawan yi”, yayin da wasu ke ganin beƙenta kan “sukar mijinta da mukarrabansa da ta sha yi.”

A Facebook kuwa gatse ake ta yi a kan saƙon, inda mafi yawa suka mayar da abin wasa, suna cewa Aisha Buhari ta shiga layin ‘yan hassada.

Wani mai sharhi a shafin Facebook Abdulaziz Tijjani ya wallafa cewa da alamar dariya a karshe: “Mamanmu ta kakkarya teburi yasin😂😂😂😂.”

Shi ma Baffa Sunusi ya wallafa a Facebook “Comrade Aisha Buhari ta shiga layin ‘yan hassada.”

Ita kuma wata mai sharhi a Facebook Arewa Queen ta wallafa: “Mama ba kyau 😂”.

A Instagram kuwa a ƙasan sakon Hausaa-Fulanii, wata mai suna talesfrom_a_northernwoman ta wallafa cikin Ingausa wato Hausa da Turanci cewa:

talesfrom_a_northernwoman: “Mun shirya wa wannan tattaunawar? Duk wani abu da take accusing din mijinta da mukarabbansa wanne ne ba gaskiya ba? Blind love (makauniyar soyayya) da kuke wa mijinta ya hana ku ganin gaskiya, Allah kadai yasan sau nawa tai masa magana behind closed doors (a daki). Amma da ta fito tai magana aka rinka tsine mata. Gaskiya dai daya ce daga kinta sai bata.

Yayin da hoori_unique_home_appliances ta ce: “To ita ma bai kamata tana wanke dirty linens insu in public ba, (wato bai kamata tana bayyana laifukansu a bainar jama’a ba.)

Wannan ba shi ne karo na farko da Hajiya Aisha Buhari ke magana kai tsaye ko a shaguɓe ga mijinta ko wasu daga cikin mukarrabansa a bainar jama’a ba.

Watakila wannan ne dalilin da ya sa kai tsaye mutane suka fassara saƙon nata da cewa Sheikh Pantami take yi wa gugar zana.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *