fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Biliyan 26 da Buhari da Osinbajo suka ware dan sayen Abinci da tafiye-tafiye sun yi yawa>>SERAP

Kungiyar dake saka ido kan mulki ta SERAP ta bayana cewa, Biliyan 26 da gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta ware da zasu kashe shi da mataimakinsa wajan tafiye-tafiye da cin abinci, sun yi yawa.

 

Kungiyar tace maimakon haka, kamata yayi a yi amfani da kudin wajan inganta kiwon lafiya na ‘yan kasa.

 

Kungiyar tace tana kura ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya aikewa da majalusar bukatar rage kudin da za’a kashe ba tare da bata lokaci ba, idan kuma ba haka ba, zasu dauki matakin zuwa kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *