fbpx
Friday, January 21
Shadow

Birthday din Halima Atete, Ali Nuhu da Aishatulhumaira sun je Landan, Hoton Kwalliyar Juma’a na Fati Washa ya jawo cece-kuce sosai

A jiya Juma’a ne wasu daga cikin taurarin fina-finan Hausa na masana’antar Kannywood suka saki kwalliyarsu ta Juma’a kamar yanda suka saba duk Mako.

Nazir Ahmad Sarkin Waka

Kamar kowace Juma’a, Shahararren Mawakin Hausa, Nazir Ahmad Sarkin waka zaune akan karagarsa me ruwan zinare ya zaki hotunan kwalliyar juma’arsa inda ya taya masoyansa murnar rabar.

Ali Nuhu da Shamsu Dan Iya

Shima Ali Nuhu, (Sarki) da Shamsu DanIya sun saki nasu hotunan na kwalliyar Juma’a.

Hadiza Gabon

Itama Hadiza Gabon ba’a barta a bayaba wajan dakin hotunan Kwalliyar Juma’a kamar yanda za’a iya gani a kasa:

Maryam AB Yola 

Tsohuwar matar Adam A. Zango,  Maryam AB Yola ma ta saki Hotuna ga masoyanta a Jiya Juma’a.

Halima Atete

Ita kuwa Halima Atete murnar zagayowar ranar haihuwarta ta yi inda abokan aikinta suka ta tayata Murna.

Ali Art work

Shima Ali Art work wanda aka fi sani da Madagwal ya yiwa masoyansa gaisuwar Juma’a.

Fati Washa

Itama Fati Washa ta saki hoton kwalliyar Juma’a inda Masoyanta suka yaba sosai.

 

Sadai a yayin da wasu suka yaba, wasu kuwa sukarta suka yi da cewa hoton bai dace dana juma’a ba.

Su Kuwa Ali Nuhu da Aisha Ahmad Idris, watau Aishatulhumaira, Landan Suka je duk da basu gayawa masoyansu abinda suka je yi ba.

 

A’isha ta saka hotunansu tare.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *