fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Biyo bayan hana bara gwamnatin Kano ta tallafawa mabarata 60

Gwamnatin jihar Kano Karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta tallafawa mata da matasa akalla 60 dabaru daban-daban na kasuwanci, biyo bayan hana bara a kan titi a jihar.

kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma, Dr Zahra’u Muhammad-Umar ita ta bayyana hakan a yayin gabatar da shirin bada tallafin ga wadanda suka ci gajiyar shirin a ranar Alhamis.

Kwamishiniyar ta ce akwai bukatar mata su kasance masu karfin tattalin arziki da kuma taimaka wa iyalansu., Tana mai bayanin cewa “Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar an zabo su ne daga kan titi da ƙarƙashin gadoji a jihar ”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *