fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Boko Haram da ISWAP sun tafka fada tsakaninsu, sun kashe juna

Kungiyar ISWAP ta kai hari kan mayakan Boko Haram a wani lamari mai kama da ɗaukar fansa a yankin Tafkin Chadi.

Hakan na zuwa ne kwana biyar bayan da wasu mayaƙan Boko Haram suka kashe mayaƙan ISWAP 24 a Tsaunukan Mandara da Gaba a garin Gwoza na jihar Bornon Najeriya, kamar yadda kafar yaɗa labaran PRNigeria ta ruwaito.

Mayaƙan ISWAP ɗin sun kai harin ne sansanin kwamandan Boko Haram Bakoura Modou a yankin Tafkin Chadin a jiya.

PRNigeria ta ce mayaƙan ISWAP ɗin sun far wa sansanin Boko Haram ɗin ne a cikin wasu kwale-kwlae masu tsananin gudu har 50.

“An kashe fiye da mayaƙan ISWAP 87 a faɗan, a cewar kafar PRNigeria.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *