fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Boko Haram sun afkawa jami’an tsaro a harin kwantan Bauna

Rahotanni sun bayyana cewa, Kungiyar Boko Haram ta Afkawa jami’an tsaro dake kan hanyar yiwa wasu membobin APC rakiya zuwa zaben kananan hukumomi da ake na jam’iyyar.

 

Suna tafiyane zuwa kananan  hukumomi Mobbar, Damasak da Abadam yayin da Boko Haram suka Afka musu a daidai Kareto.

 

Lamarin yayi sanadiyyar kisan wasu mutane ciki hadda jami’an tsaro kamar yanda Vanguard ta ruwaito.

 

Dole aka hakura da tafiyar aka koma gida. Kokarin jin ta bakin Hukuma kan lamarin ya faskara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *