fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Boko Haram Sun kashe mutane akalla 30 a harin da suka kai jihar Borno

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kai ziyara ta musamman a garin Auno domin ganin barnar da ‘yan Boko Haram suka yi a
wani mummunan hari da suka kai. Wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tare da asarar dukiya.

An kai harin ne a kauyen Auno da misalin karfe 10:00 na daren jiya, inda ‘yan ta’addan suka kashe mutane 30 tare da kona motoci, gidaje, shaguna da sauransu.
A yayin ziyarar jaje, Gwamna Zulum ya taya al’ummar yankin jaje na faruwar lamarin. Ya kuma yi kira gare su su zama masu lura da sanya ido akan duk wani motsi da basu gane masa ba.
Gwamna Zulum ya kuma yi ķira ga sojoji da su kara karfin ayyukan su, a wannan yanki
domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Borno baki daya.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *