fbpx
Monday, October 25
Shadow

Boko Haram sun kashe Sojojin 7 a harin kwantan Bauna

Rahotanni daga jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayakan Iswap sun yi wa sojojin kasar kwantan bauna a yankin Marte-Dikwa.

Jaridar PRNigeria da ke da kusanci da sojojin Najeriya ta ce sojoji bakwai da ‘yan banga hudu aka kasha bayan Iswap ta dasa abubuwan fashewa ne domin ayarin soji da ke kan hanyar Maiduguri daga Marte.

Ayarin motocin sojojin na rakiyar sojojin da aka ba su izinin fita daga yankin Marte, a cewar jaridar.

Ta ce wani jami’in leken asiri ya ce an yi wa sojojin kwanton bauna ne a kusa da kauyen Ala da ke tsakanin garin Marte da Dikwa.

“Mayakan sun boye kusa da wurin suka bude wa sauran ayarin wuta, wanda ya kai ga rasa ran akalla sojoji bakwai da ‘yan banga hudu da ke cikin ayarin.”

Sai dai babu wata sanarwa daga rundunar sojin Najeriya game da al’amarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *