fbpx
Friday, January 21
Shadow

Boko Haram sun sace jamo’in gwamnati

Aƙalla jami’ai biyar na gwamnatin jihar Borno ƴan ƙungiyar da ke iƙirarin jihadi ta ISWAP suka sace a jihar.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa an sace jami’an ne da ƙarfi da yaji a lokacin da suke kula da aikin wata hanya da ake ginawa tsakanin Chibok zuwa Damboa.

Lamarin ya faru ne a kusa da Wovi, wani ƙauye da ke a yankin Ƙaramar Hukumar Chibok.

Ko a cikin Nuwambar nan sai da ƴan ISWAP ɗin suka kashe wani janar ɗin Najeriya da wasu sojoji uku.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *