fbpx
Monday, November 29
Shadow

Boko Haram sun saci ‘yan mata 22 daga jihar Naija inda suka ce aurensu zasu yi

Mayakan Boko Haram sun shiga kauyen Kurebe dake jihar Naija inda suka sace ‘yan mata 22.

 

Wanda suka sace din suna tsakanin shekaru 15 zuwa 17. Majiyar Leadership ta ruwaito cewa, mayakan sun ce auren wadannan yara zasu yi.

 

Shugaban kauyen yace tun kamin zuwan ‘yan Bindigar,  sun aiko da sako cewa a cire yaran daga makaranta dan zasu zo su daukesu su auresu.

 

Yace kuma sai gashi sun tabbatar da abinda suka ce ba tare da koda jami’in tsaro daya ba.

 

Yace ‘yan Bindigar na shiga garinsu su yi abinda suka ga dama kuma sun kai kara wajan jami’an tsaro amma babu wani matakin da aka dauka akan lamarin.

“They operate freely but when they identify a stranger in the community, they usually feel threatened; they either plan for the abduction of the stranger or chase the person away; we reported several times to the authorities,” he said.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *