fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Boko haram ta kai sabon hari jihar Yobe

Rahotanni daga jihar Yobe na cewa mayaƙan Boko Haram sun kai hari ƙauyen Babban Gida da ke ƙaramar hukumar Tarmowa a jihar Yobe.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa tun ranar Alhamis maharan suka sanar da cewa za su kai harin.

Ya kuma bayyana cewa sun kai harin ne da misalin ƙarfe biyar na yamma inda har kusan ƙarfe takwas na dare suna jiyo ƙarar harbe-harben bindiga,

Wata majiyar ta daban ta shaida wa BBC cewa maharan sun zo a motoci guda biyar ne kuma sun fara auka wa sansanin jami’an tsaron Najeriya kuma jami’an sun fatattake su.

Daga bisani ne kuma suka shiga yankin da mutane ke zaune suka ci gaba da harbe-harbe.

Ya zuwa yanzu dai babu rahoton asarar rai ko kuma jikkata.

Babu wanda ya sani ko yanzu ma kayan abinci suka zo ɗauka kamar wancan lokacin da suka kai irin wannan harin aka kore su kuma aka ƙwace motarsu guda.

Kawo yanzu hukumomi ba su ce komai ba kan harin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *