fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Boko Haram ta kwace garuruwa 500 a jihar Neja – Shugaban karamar hukumar shiroro

Mayakan Boko Haram sun karbe garuruwa sama da 500 a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, a cewar shugaban Shiroro Suleiman Chukuba.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a, 30 ga watan Satumba, Chukuba ya ce yanzu haka akwai unguwanni 8 da ke karamar hukumar yanzu suna karkashin hare -haren Boko Haram.

Ya ce yankunan da abin ya shafa sune Manta, Gurmana, Bassa-Kokki, Allawa, Kurebe, Kushaka, Kwati, Chukuba da Galadima Kogo.

Ya ce: “Suna neman goyon bayan al’ummomin garuruwan ne ta hanyar gaya musu cewa suna da makamai da kudi da za su ba su don su taimaka musu wajen yakar gwamnati.

Shugaban majalisar yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara tura jami’an tsaro yankin domin yaki da masu tada kayar baya da suka maida Shiroro gidan su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *