fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Buba Galadima na barazanar kafa sabuwar jam’iyyar siyasa da za ta yaƙi tsaro a Najeriya

Wani fitaccen ɗan siyasa a Najeriya, Alhaji Buba Galadima ya yi barazanar kafa sabuwar jam’iyya da a cewarsa za ta kawo maslaha ga dumbin matsalolin da Najeriya take ciki a yanzu, musamman tsaro.

Alhaji Buba Galadima ya bayyana haka ne bayan wani taro da ƙungiyar tuntubar juna ta National Consultative Front ta gudanar kan halin da ƙasar ke ciki.

“Muna da dama mu hada kanmu mu bijiro da wata tafiya wadda za ta tabbatar da shugabanni na kirki wadanda za su yi aiki don al’umma ba don aljihunsu ba,”

“Muna da dama da za mu iya tsayar da mutumin da za mu iya rantsar da shi da zai yi aiki da kundin tsarin mulkin kasar nan ko kuma mu gyara kundin tsarin mulkin kasar ta hanyar da al’umma suna da bakin da za su fada dole a bi.” . in ji Buba Galadima.

Baya ga matsalar tsaro, Kungiyar ta kuma tattauna kan matsalolin da suka shafi tattalin arziki tare da kuma gabatar da wasu shawarwari.

Buba Galadima ya bayyana wa BBC wasu shawarwarin da yake ganin za su kawo gyara a kasar kamar bai wa kowane mataki damar tafiyar da mulki ba tare da karen tsaye ba.

A cewarsa babbar matsalar da ake fuskanta a kasar ita ce yadda wasu matasa suka kasance kara zube ba tare da samun aikin yi ba abin da ke sa wasunsu daukar makamai “suna tsare hanya suna tare masu tafiya”.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *