fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Budurwa ta sacewa dansandan Najeriya Bindigarsa da Dubu 50 bayan da yayi lalata da ita a Ofis

An kama wata mata, Jennifer Madueke bisa zargin ta sacewa dansanda, DPO, CSP Adegoke Akinlade bindigarsa ta aiki.

 

Matar da Akinlade sun taba yin soyayya a baya wanda daga baya aka masa canjin wajan aiki zuwa Legas.

 

Amma aka sake dawo dashi Legas din. Ya hadu da ita suka sake komawa soyayya. Daga nan ne sai ya kaita Ofishinsa ya kwana da ita, kamar yanda wata majiya ta bayyanawa, Punchng.

 

Saidai daga baya ya sake gayyatar ta inda data zo yasa aka kamata aka daure bisa zargin ta sace masa Bindiga.

 

Hakan yasa aka rika gana mata azaba, har wajan wani boka ya kaita kuma ya tabbatar masa cewa itace ta yi satar, saidai Jennifer ta karyata wannan zargi.

 

Amma daga baya da azaba ta mata yawa, ta amsa laifin.

 

Saidai DPO Akinlade yace bai yi lalata da Jennifer ba kumama har da dubu 50 ta sace masa. Yace Tabbas tsohuwar budurwarsa ce amma sun dade da rabuwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *