fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Budurwar ta hada bakibda saurayinta yayi garkuwa da ita dan su samu kudi

‘Yansanda a jihar Ekiti sun kama wata matashiya me shekaru 16, Abimbola Suluka da saurayinta, Oluwaseun Olajide bisa zargin yin garkuwa da mutane ta karya dan su nemi kudi.

 

Matashiyar ta hada baki da saurayin nata da kuma wasu abokansa 2 dan su saceta ta samu kudi.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Sunday Abutu ya bayyana cewa, ‘yar uwar yarinyar ce ta kai musu karar cewa, an sace ‘yar uwarta.

 

Ya bayyana cewa sun nemi a basu 500,000 amma bayan da suka bayar da Asusun bankin da za’a zuba kudin a ciki, an gano me asusun inda kuma ya kai jami’an tsaron otal din da yarinyar da saurayinta suke.

 

Yatinyar tace tana son samun kudi ne dan ta gudu daga jihar saboda ita ‘yar Fim take son zama amma Mahaifiyar ta tace sai ta zama Likita.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *