Fadar shugaban kasa, ta bayyana cewa, babu inda gwamnatin tarayya ta taba Alkawarin cewa zata matar da Naira daraja daidai da Dala.
Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana cewa, jitajitar da ake yadawa cewa shugaban kasar ya fadi haka ba da gaske bane.
A labarai da hutudole.com ya samo muku daga Hirar da Channelstv ta yi da Adesina lokacin da yake amsa wannan tambaya da aka masa, ya kekashe kasa yace wannan magana karyace tsagwaranta, ba’a yi ta ba.
A baya dai, hutudole.com ya kawo Labarin siyasa daga jihar Sokoto dake cewa jam’iyyar PDP ta kashe gaba dayan kujerun kananan hukumomin da aka yi a jihar.
Adesina ya kuma kara da cewa a baya, Lai Muhammad, Watau Ministan Yada labarai ma ya karyata wannan magana inda yace idan akwai me Bidiyon inda shugaban kasar ya fadi haka, ya zo dashi.
“It does not exist, it is fake, it is false, it is apocryphal, it doesn’t exist” Mr. Adesina insisted while appearing as a guest on Channels Television’s Sunday Politics.
Adesina said the minister of information, Alhaji Lai Mohammed has debunked the claim severally and challenged anyone with clips and publications to make them available.