fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Buhari da APC ne suka lalata Najeriya ba ruwanmu>>PDP suka mayarwa da Jega martani

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa laifi ne babba wanda kuma ba za’a yafeshi ba yanda Farfesa Attahiru Jega,  tsohon Shugaban INEC ya hadasu da APC.

 

PDP tace a zamanin mulkinsu sun kawo abubuwan ci gaba amma mulkin APC banda bakar wahala da kuncin Rayuwa babu abinda ya kawowa ‘yan Najeriya.

 

PDP tace abin takaici be yanda Farfesa Jega a matsayinsa na me ilimj ya kasa banbance irin mulkin da suka yi na ci gaba da wanda APC ke yi na koma baya.

 

Dan haka ta yi kira ga Jega ya daina hadasu da APC. PDP tace har yanzu ‘yan Najeriya basu manta da irin rawar da Jega ya taka ba wajan kawo APC akan mulki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *