fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Buhari ya aika sakon taya murna ga Sakataren Majalisar Dinkin Duniya da mataimakiyarsa Amina Muhammad kan sake nada su karo na biyu

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya taya Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, murnar sake nada shi karo na biyu a kan mulki.

Ya kuma taya mataimakiyar Sakatare-janar haifaffiyar Najeriya, Amina Mohammed, kan sake nada ta.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken ‘Shugaba Buhari na taya sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, da Amina Mohammed murnar rike aiki a karo na biyu.’

Sanarwar da aka karanta a wani bangare “Shugaba Buhari na taya Sakatare-Janar da Mataimakiyar Sakatare Janar, wadda ta kasance tsohuwar Ministan Muhalli a Najeriya, saboda karramawar duniya da damar da za ta yi wa dan Adam aiki tare da gogewa, yana mai dogaro da cewa burinsu na inganta zaman lafiya, rage talauci, inganta kiwon lafiya da karfafawa mutane da yawa za su samu karin sauri da sakamako. ”

Buhari ya bayyana kwarin gwiwar cewa tsawaita wa’adin nata a ofis zai karfafa gwiwar mata da ‘yan mata, musamman ma a Afirka da Nijeriya, don yin burin samun sabon matsayi na jagoranci, sa buri fiye da iyakokin kasashen su da kuma koyo daga sadaukarwar ta na ganin rayuwar ta canza zuwa mafi kyau.

Ya kuma yaba wa tsohuwar ministar kan irin gudummawar da ta bayar wajen ci gaba, a cikin gida da waje, yana mai addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba ta lafiya, karfi da kuma karin hikima don wannan tafiya da ke tafe.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *