fbpx
Monday, November 29
Shadow

Buhari ya ba ‘yan Najeriya Kunya>>Kunguyar Dattijan Arewa

Kungiyar dattijan Arewa da ake kira da Northern Elders Forum a Turance ta yi zama a Ranar Lahadi data gabata inda ta fitar da matsayar cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gaza musamman a akan harkar tsaro.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Dr. Hakeem Baba Ahmad ne ya karanto sanarwar bayan taron kungiyar ga manema labarai inda yace tabarbarewar harkar tsaro ta kara muni a karkashin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Yace talauci musamman a Arewacin Najeriya ya taimakawa kara munin matsalar tsaro.

Yace akwai alaka me karfi tsakanin Talauci da matsalar tsaro inda yace talauvi na kara zurfafa matsalar.

Yace kamin zaben shekarar 2019, kungiyar ta dattijan Arewa ta gargadi mutane cewa shugaba Buhari bashi da kwarewar da zai kai Najeriya ga ci ta hanyar tattalin Arziki da tsaro. Yace gwamnatin ta Buhari bata ma san ta yadda zata magance matsalar ba kuma abin takaicin shine shugaban ko dai yayi kunnen uwar shegu akan wannan matsala ko kuma yaki amincewa ma akwai ta.

Da yake magana akan zaben 2023 yace wanda zai kawo ci gaba ne zasu zab


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *