fbpx
Monday, November 29
Shadow

Buhari ya taya Sarkin Musulmi murnar cika shekara 15 kan gadon sarauta

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III murnar cika shekara 15 kan gadon sarauta.

Shugaban,cikin sanarwar da Malam Garba Shehu ya fitar ya bayyana Sarkin a matsayin “mai gina zaman lafiya da jajircewa ga aikinsa, kuma shugaban da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kyautata rayuwar al’umma.”

Buhari ya yi wa Sarkin Musulmi fatan samun wasu shekaru masu yawa kan matsayinsa tare da ci gaba da aikin tabbatar da zaman lafiya tsakanin addinai da ƙabilu a sassan Najeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *