fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutane a jihohin Benue da Anambra

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutum 11 a Ƙaramar Hukumar Gwer West ta jihar Binuwai da kisan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da wasu gungun mutane suka tare su a hanya suka yi.

A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya yi tur da kisan mutane a Anambra.

“Ba za mu amince da kisan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba daga koma wanene,” a cewarsa.

Shugaban ya ce ƙiyayya da hamayya su ne ke haifar da irin waɗannan kashe-kashen. Ya kuma ce idan aka sa wa irin waɗannan mugayen mutane ido, lallai za su lalata dokokin ƙasar.

Shugaban ya buƙaci shugabannin gargajiya da na addini sun yi amfani da matsayinsu wajen shawo kan mabiyansu don taimaka wa gwamnati a ƙoƙarinta na tabbatar da zaman lafiya.

Shugaba Buhari ya gargaɗi ƴn Najeriya kan ɗaukar doka a hannayensu da sunan ramuwa saboda “babu wanda zai yi nasara a tashin hankali”.

Haka kuma, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mutanen da suka rasu da gwamnati da al’umar jihohin Binuwai da Anambra.

Ya jinjina wa ƴan sanda da sauran jami’an tsaro bisa rawar da suka taka wajen gaggauta shawo kan rikicin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *