fbpx
Friday, January 21
Shadow

Buhari zai duba Maslahar ‘yan Najeriya kamin ya saki Nnamdi Kanu>>Abubakar Malami

Babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami ya bayyana cewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai duba maslahar ‘yan Najeriya kamin ya saki shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

 

Ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi a gidan talabijin na NTA.

 

Malami ya kara da cewa shugaba Buhari zai duba amfanin Saki ko rashin sakin Kanun ga mafi yawancin ‘yan Najeriya amma ba wasu tsiraru ba.

 

Dattawan Inyamurai dai sun kaiwa shugaba Buhari ziyara a fadarsa dake Abuja inda suka nemawa Kanu Afuwa.

 

Sun nemi shugaba Buhari ya saki Kanu ba tare da sharadi ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *